in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Mozambique ya kaddamar da filin saukar jiragen sama na Maputo da Sin ta taimaka wajen ginawa
2012-10-18 10:46:40 cri

Shugaban kasar Mozambique Armando Emilio Guebuza a ran 17 ga wannan wata ya jagoranci bikin kaddamar da wani sashe na filin saukar jiragen sama a birnin Maputo wanda Sin ta ba da taimako wajen gina shi.

Jakadan kasar Sin dake kasar, Huang Songpu da wasu manyan jami'an kasar Mozambique sun yi wa Armando Emilio Guebuza rakiya yayin ziyara da suka kai na ganin ginin.

A cikin jawabinsa, Armando Emilio Guebuza ya nuna godiya matuka ga kamfanin kasar Sin dangane da bada taimakon, sannan ya nuna gamsuwarsa kan kokarin da ma'aikatan kasashen biyu suka yi.
Yana mai nuna fatan cewa kara dankon zumunci da kuma zurfafa dangantakar hadin kai ta abokantaka tsakanin kasashen biyu da kuma al'ummarsu.

A cikin jawabinsa, Huang Songpu ya ce, sabon ginin tamkar wata shimfida ce da za ta hada kasar Mozambique da kasar Sin har ma da sauran kasashen duniya waje guda. Sin na fatan kasashen biyu za su kara hadin kai wajen samun ci gaba mai amfani nan gaba.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China