A ranar 22 ga wata, dakarun dake adawa da gwamnati Renamo sun kai hari ga hukumar 'yan sanda da ke tsakiyar kasar, inda suka sanar da cewa, dalilin da ya sa aka dauki wannan mataki shi ne don mayar da martini game da mamaye sansanin jagoransu da sojojin gwamnatin suka yi, a sa'i daya kuma, dakarun Renamo sun bayyana dakile yarjejeniyar samar da zaman lafiya da aka daddale tsakaninsu da gwamnatin Mozambique.
Ban da wannan kuma, halin da ake ciki a kasar Mozambique ya kawo damuwar wasu kasashen da ke makwabtaka da ita. Sabo da kasar Mozambique, babbar hanyar sufurin makamashi da kayayyaki ne ta Zimbabwe, kasar Zimbabwe ta nuna damuwa ga halin da ake ciki a kasar Mozambique, tare da yin Allah-wadai da aika-aikar dakarun Renamo. Ita ma a wannan ranar kasar Afrika ta Kudu ta bayyana cewa, halin da ake ciki a Mozambique zai haifar da cikas ga aikin samar da zaman lafiya a wannan yanki.(Bako)