Shugaban kasar Mozambique Armando Emilio Guebuza ya bayyana a jiya Lahadi 20 ga wata cewa, gwamnati ba zai daina bincike kan hadarin jirgin sama dake dauke da tsohon shugban kasar Samora Moisés Machel ba, wanda ya faru a shekarar 1986 kuma ya girgiza dukkan nahiyar Afrika.
Armando Emilio Guebuza ya fadi haka ne yayin da ya halarci bikin ranar cika shekaru 27 da rasuwar Samora Moisés Machel da aka shirya a arewacin kasar.
An ba da labarin cewa, a ran 19 ga watan Oktoba na shekarar 1986, a kan hanyar sa na dawowa gida, jirgin sama da marigayi Samora ya ke ciki ya fadi a kan wani dutse dake gabashin bakin iyakar kasar Afrika ta kudu, abin da ya hallaka Mr Samora Moisés Machel da sauran mutane fiye da 20 dake cikin jirgin.
Kafar yada labaru ta kasar ta ba da labarin cewa, dalilin da ya sa jirgin saman musamman na tsohon shugaban kasar ya fadi shi ne, sabo da ya samu wata alama kuma ya karkatar hanyar da yake bi. (Amina)