Mista Vaquina wanda ya fadi haka ne a wani shirin da gidan telabijin da radiyon kasar da na rediyon kasar suka gabatar, inda ya ce gwamnatin kasar tana bincikenazari kan ko za a kafa asusun ko a'a, kana gwamntin za ta yi kokarin tsayar da wani kudurin da yamai dacewa don taimakawa kasar fitowa daga wani mawuyacin halin da ta tsunduma ciki.
A cewar Mista Vaquina, babban aikin dake gaban kasar Mozambique shi ne kokarin fid da kanta daga kangin talauci. Don ganin an raya zaman al'umma da tattalin arzikin kasar, ana bukatar kara gina kayayyakin more rayuwa irin su makarantu, hanyoyin mota, da dai makamantan sukanta. Amma kafin a cimma burin da aka sanya a gaba, tilas ne a samu kudin da ake bukata.
Firaministan ya kara dayi bayanin cewa, masana ilimin tattalin arziki na kasar da na kasashen waje suna ganin cewa, idan an yi amfani da kudin da ake samu ta hanyar sarrafa albarkatun kasa don kafa wani asusun raya kasa, sa'an nan an dingaka ware kudi don gina kayayyakin more rayuwa a kasar, wacce lalle ta wannan hanya, ne za a amfanawa daukacin jama'ar kasar Mozambique. Haka zalika, asusun zai iya tallafawa shirin kasafin kudin kasar, don rage dogaro kan tallafi daga kasashen waje. (Bello Wang)