Yawancin fannonin da kasar Sin ta zuba jari a kai sun hada da gine-gine, shimfida hanyoyin mota da gadoji, da kuma samar da siminti.
Kawo yanzu dai kasar Sin ta riga ta kammala akasarin ayyukan gina sabbin gine-ginen gwamnatin kasar, kamar su cibiyar taruruka ta kasa da kasa ta Joaquim Chissano, ginin kotun tsarin mulkin kasar da manyan kotunan kasar, gami da dakunan ofisoshin ma'aikatar harkokin waje da ta yawon shakatawa na kasar.
Haka kuma kasar Sin ta yi kwaskwarima ga filin jiragen sama na Maputo, yayin da take cikin shirin shimfida wata gada a kan tekun Indiya domin hada Matupo, babban birnin kasar Mozambique da sabuwar unguwar Katembe ta birnin tare, wanda za a kashe kudi Dala miliyan 70.
Yanzu kasar Sin na kokarin shimfida hanyoyin da ke haduwa da juna domin warware matsalar cunkuson motoci da ke addabar birnin Maputo .(Kande Gao)