in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Mozambique ya yaba game da manufar kasar Sin kan kasashen Afirka
2012-10-04 16:42:07 cri
A daren ranar Laraba 3 ga wata, Shugaban kasar Mozambique, Armando Emilio Guebuza ya bakunci ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Mozambique tare da iyalansa bisa goron gayyatar jakadan Sin a kasar, Huang Songfu.

A yayin wannan ziyara, Shugaba Guebuza ya yi tsokaci a kan abubuwan da suka faru tsakaninsa da abokansa Sinawa bayan yakin neman samun 'yancin al'ummar Mozambique, da kuma dankon zumunci dake tsakaninsu, inda ya ce, akwai dadadden zumunci tsakanin kasashen Mozambique da Sin da kuma jama'arsu baki daya, wanda yanzu haka dangantakar abokantaka da hadin gwiwa tsakaninsu na bunkasa yadda ya kamata.

Ban da haka kuma, Shugaba Guebuza ya yaba a kan manufofin da gwamnatin kasar Sin take dauka kan kasashen Afirka, musamman ma a kasar Mozambique, inda ya lura da cewa, Sin na kokarin kafa dangantakar abokantaka da hadin gwiwa tsakaninta da kasashen Afirka, da suka hada da Mozambique cikin tsanaki ba tare da wani sharadi ba.

Dadin dadawa, Shugaban ya yi bayanin cewa, hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu ya riga ya sami ci gaba a fannin aikin noma. Kuma bisa taimakon kasar Sin, ba shakka kasar Mozambique za ta iya samar da abinci da kanta, kuma nan gaba kasar za ta iya fitar da abinci zuwa kasashen waje, ta yadda za ta ba da gudummawa wajen daidaita matsalar karancin abinci a duniya baki daya.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China