Kwayoyin dabi'ar hallitar mutum su ne suke sarrafa yanayin jikin mutum wato Biological clock. Yanayin jikin mutum ya dan sha bamban da awoyi 24 na ko wace rana, amma jikin mutum shi kansa kan kyautata yanayinsa bisa ga hasken rana da kuma cin abinci, ta yadda
Nazarin da aka yi a baya ya nuna cewa, matsalar yanayin jikin mutum kan haddasa karuwar yawan kibar da ke taruwa a jikinsa da kuma kamuwa da ciwon sukari. Gwaje-gwajen da masu kimiyya da ke aiki a jami'ar Waseda ta kasar Japan suka yi kan dabbobi sun shaida cewa, cin abinci ta hanyar da ta dace zai iya taimakawa wajen yin rigakafin karuwar yawan kibar da ke taruwa a jikin mutum. An kaddamar da sakamakon wannan nazari a yayin taron shekara-shekara na kungiyar kula da harkokin kiba ta kasar Japan a hukumance.
Masu nazarin na kasar Japan sun ciyar da kananan beraye sau daya a ko wace rana, daga baya sun gwada yanayin kwayoyin dabi'ar hallitarsu da ke kodarsu da hantarsu, tare da yin bincike kan yanayin jikinsu. A karshe sun gano cewa, idan sun ciyar da berayen da karfe 7 na safe, tsakar rana da kuma karfe 7 na yamma bisa agogon dan Adam, to, lokacin da ke tsakanin abincin dare da karin kumallo na kashegari ya fi tsawo ga berayen a duk rana guda, inda ba su ci kome ba. Bayan wannan tsawon lokaci na rashin cin kome, karin kumallo na kashagari ya iya kyautata yanayin jikin berayen daidai. To, in mun dauki jikin bera ko na dan Adam a matsayin halitta mai dauke da wani irin agogo, wanda ke sarrafa yadda jikin ke gudanar da ayyukansa bisa wani tsari na musamman a kuma ko wane lokaci. Ta haka ma iya cewa, karin kumallo yana taka muhimmiyar rawa wajen daidaita wannan agogon da ke jikin berayen a rana guda.
Amma idan an dage ciyar da berayen abincin dare har zuwa karfe 10 na dare, to, berayen za su gudanar da harkoki a makare har awoyi 2 zuwa 3. Masu nazarin na ganin cewa, dalilin da ya sa haka shi ne domin tsawon lokacin da ke tsakanin abincin rana da abincin dare ya kusan yi daidai da tsawon lokacin da ke tsakanin abincin dare da karin kumallo na kashagari, lamarin da ya haifar da matsala a yanayin jikin berayen. Idan an ciyar da berayen da karfe 7 na dare da kuma karfe 10 na dare, to, berayen kan gudanar da harkoki a makare har awa daya da rabi zuwa awoyi biyu.(Tasallah)