in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cin tafarnuwa a yayin da ake cin nama na da kyau
2013-02-06 09:21:33 cri
Abincin da aka dafa tare da nama yana da dadin ci, kuma yana hade da sinadarai masu gina jiki da dama, saboda haka irin wannan abincin ya fi samun karbuwa daga mutane. Amma, idan ka ci tafarnuwa a yayin da kake cin wannan abinci, to zai taimake ka wajen kara sha'awar abincin, da kuma samun koshin lafiya. To, masu sauraro, a cikin shirinmu na yau za mu kawo muku wani bayani game da wannan abincin.

Ko akwai mutanen da ke kewayenku da ke son cin nama sosai, har ma suna sha'awar cin nama a ko wace rana? Ni ma ina da wasu abokaina da ma'aikata masu sha'awar cin nama matuka, idan ba su ci nama ba, za su ji kamar ba su ci abinci ba.

Akwai wani karin magana na kasar Sin da ke cewa, 'Idan ba a ci tafarnuwa a yayin da ake cin nama ba, to abubuwa masu gina jiki da ake bukata za su ragu da kimanin rabi'. Cin nama tare da tafarnuwa zai sanya mutane su kara sha'awar cin abincin, kana da samun sinadarai masu gina jiki mafi yawa daga naman.

Bisa nazarin da aka yi an ce, a cikin abinci kamar nama, musamman ma nama maras kitse suna kunshe da sinadarin Vitamin B1 da yawa, wadannan sinadarin ba sa dadewa a cikin jikin mutum, idan jikin mutum bai iya rike sinadarin cikin lokaci ba, to za a fitar da shi ta hanyar yin fitsari.

Tafarnuwa na kunshe da wasu sinadarai na musamman, bayan da suka gamu da sinadarin Vitamin B1 hakan na iya haifar da wani irin sinadarin da ke iya kara yawan sinadarin Vitamin B1 har ya ninka sau 4 zuwa 6. Ban da wannan kuma, wannan irin sinadarin na iya taimaka wa wajen tsawaita lokacin kasancewar sinadari Vitamin B1 a cikin jikin mutum, kana da kara yawan sinadarin Vitamin B1 da ke jikin mutun, hakan na taka muhimmiyar rawa wajen kawar da gajiya, da kara karfin jiki.

Bugu da kari, Sinawa su kan mai da tafarnuwa a matsayin wani muhimmin abinci da magani wajen rigakafin wasu cututtuka, har ma ana harhada wasu magunguna da sinadaran dake cikin tafarnuwa, wadanda ke da amfani wajen kawar da kwayoyin cuta da kumburi, da kuma maganin cutar sankara.

Gaskiya ne tafarnuwa na da amfani sosai ga koshin lafiya, saboda haka yana da kyau a ci tafarnuwa a yayin da ake cin nama a zaman rayuwarmu na yau da kullum, ba kawai wannan zai taimaka wajen kawar da wari na nama ba, har ma zai taimaka wajen kara bugun jini, da kawar da gajiya, kana da kara yawan sinadarai masu gina jiki da jikin mutum ke bukata.(Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China