in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shan bakin shayi na iya taimaka wa mutane yaki da ciwon sukari
2013-09-02 16:42:08 cri

Masu karatu, an tabbatar da cewa, shan shayi na da amfani sosai ga lafiyar mutane a fannoni daban daban. Sakamakon wani nazari mai dumi-dumi da aka bayar a kwanan baya ya shaida mana cewa, a cikin wasu kasashe inda mutane ke shan bakin shayi kullum, yawan wadanda suke kamuwa da ciwon sukari ya yi karanci.

Mujallar kamfanin buga mujallolin ilmin likitanci na kasar Birtaniya ne ta wallafa wannan rahoto da ke cewa, masu nazari daga kasar Switzerland sun tattara bayanai dangane da batun shan bakin shayi a wasu kasashen duniya. Sakamakon ya nuna cewa, mutanen kasar Ireland sun fi sha'awar shan bakin shayi, kuma matsakaicin yawan ganyayen shayin da ko wane mutum a kasar Ireland ya kan sha a ko wace shekara ya wuce kilo 2. Haka kuma, a kasashen Birtaniya, Turkey da Rasha, su ma mutanensu suna sha'awar shan bakin shayi. A kasar Sin kuma ko da yake tana da yalwar gangayen shayi, amma mazaunan kasar sun fi sha'awar shan koren shayi a maimakon bakin shayi, wanda hakan ke nuna tana baya a cikin jerin kasashen da ke shan bakin shayi, kamar dai matakin da su ma kasashen Korea ta Kudu da Brazil suke kai.

Ban da haka kuma, masu nazarin sun yi bincike kan yawan mutane masu kamuwa da ciwon kansa, ciwon zuciya, ciwon sukari da dai makamantansu a wadannan kasashe. Bayan da suka kwatanta adadin da suka samu, sun gano cewa, a kasashen da mutane ke shan bakin shayi, yawan wadanda ke kamuwa da ciwon sukari ya yi karanci.

Masu nazarin sun kuma bayyana cewa, nazarinsu ya bayyana dangantakar da ke tsakanin al'adar shan bakin shayi da kuma yawan masu sha'awar shan bakin shayi da suka kamu da ciwon sukari kawai, ta yadda hakan zai ba su damar ci gaba da nazari kan yadda shan bakin shayi ke iya yin tasiri ga kamuwa da ciwon sukari.

A zahiri, baya ga ciwon sukari, sinadarin Caffeine da ke cikin shayi da kofi yana iya sassauta illolin da cutar Parkinson ke haifarwa, kuma yana iya bai wa masu fama da cutar karfin ci gaba da motsi. Duk da haka ana bukatar ci gaba da irin wannan nazari cikin dogon lokaci. Masu nazari suna ganin cewa, ya zama dole a yi nazarin yiwuwar yin amfani da sinadarin Caffeine wajen shawo kan cutar Parkinson. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China