in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Vitamin D ta iya fama da ciwon sankara
2013-06-04 15:34:08 cri
Bincike daga cibiyar nazarin ciwon sankara ta kasar Faransa ya bayyana a kwanan baya cewa, mai yiwuwa ne karancin sinadarin vitamin D a cikin jikin dan Adam na iya haifar da karuwar yawan kamuwa da ciwon sankara. Masu ilmin kimiyya sun shawarci mutane da su karfafa samar da sinadarin vitamin D a jikinsu ta hanyar shan hasken rana, ta yadda za a magance kamuwa da ciwon sankara.

Masu ilmin kimiyya na wannan cibiyar kasar Faransa sun yi bincike kan maza dubu 48 har na tsawon shekaru 14. Sun yi nazari kan halin da jikunan mutane suke kasancewa ta fuskar samun sinadarin vitamin D da kuma dukkan sanadaran jiki da na tunani da suke ba da tasiri kan mutane wajen shan hasken rana, kamar wanda ke da kiba, ba ya son jin zafi, wani kuma ba ya son fatarsa ta canja zuwa baki, ta haka ba su shan hasken rana da yawa.

A karshe dai, sun gano cewa, idan mutum ya samu sinadarin vitamin D da yawansa ta kai wanda ake bukata bisa ga lissafin masanan kimiyya na duniya International Unit wato IU dubu daya da dari 5 a cikin jikinsa a ko wace rana, to, za a rage yawan yiwuwar kamuwa da ciwon sankara da kashi 17 cikin dari, kana kuma yawan mutuwar masu fama da ciwon sankara zai ragu da kashi 29 cikin dari.

Masu ilmin kimiyyar sun kuma nuna cewa, vitamin D da yawanta ya kai International Unit wato IU dari 4 na iya biyan bukatun mutune, wanda mutane su kan samu ta hanyar cin abinci a ko wace rana, sai dai ya yi kadan sosai, in an kwatanta ta da wadda aka samu ta hanyar shan hasken rana a ko wace rana. A zarihi kuma, idan wani mai koshin lafiya ya sha hasken rana har tsawon mintoci 30 a ko wace rana, to, za a samar da vitamin D da yawanta ta kai misalin International Unit wato IU dubu 20 a cikin jiki. Saboda haka, shan hasken rana, wata muhimmiyar hanya ce da mutane suke bi wajen samun isasshiyar vitamin D, mai yiwuwa ne ya taka rawa wajen raguwar yawan masu kamuwa da ciwon sankara.

Saboda sakamakon nazarin da suka samu, masu ilmin kimiyyar sun kara yin imanin cewa, sinadarin vitamin D na iya yaki da ciwon sankara. Amma sun tunatar da cewa, kada a dogaro da shan magunguna domin samun sinadarin vitamin vitamin D. Shan magungunan fiye da kima yana kawo wa lafiyar mutane illa. Ban da wannan kuma, wajibi ne tsawon lokacin shan hasken rana ya dace da ko wane mutum.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China