in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shayar da jariransu da nono kan taimaka wa masu juna biyu da ke fama da ciwon sukari rage barazanar sake kamuwa da ciwon bayan haihuwa
2013-09-02 16:47:42 cri
Mutane suna kara fahimtar cewa, shayar da jarirai nonon uwayensu mata kan amfana ga lafiyar jariran. A gaskiya kuma, hakan yana kawo wa iyaye mata alheri.

Wani nazarin da aka yi a kwanan baya a kasar Jamus ya shaida cewa, bisa sakamakon nazarin da aka dauki tsawon lokaci ana yinsa, an gano cewa, shayar da jarirai nonon iyaye mata na taimakawa wajen rage wa matan da suka kamu da ciwon sukari sakamakon samun juna biyu barazanar sake kamuwa da ciwon na nau'in 2 a nan gaba. Ciwon sukari na nau'in 2 shi ne ake iya shawo kansa ta hanyar amfani da shan magani, a maimakon yin allurar sinadarin insulin.

Reshen hadaddiyar cibiyar nazari ta Helmholtz da ke birnin Munich na kasar Jamus ya gabatar da sakamakon nazarin da aka ambato a kwanan baya, tare da cewa, matan da suka yi watanni fiye da 3 suna shayar da jariransu nonon suna iya cin gajiya. Sanin kowa ne cewa, a lokacin da mata suke da juna biyu, su kan samu rashin daidaito a jikunansu, lamarin da ya sanya su kamu da ciwon sukari. Ko da yake watakila yawan sukarin da ke cikin jininsu zai koma yadda ya kamata bayan sun haifi jarirai, amma wadannan mata sun fi fuskantar barazanar kamuwa da ciwon sukari na nau'in biyu. Adadin kididdigar da aka samu ya nuna cewa, kusan rabin matan da suka kamu da ciwon sukari sakamakon samun juna biyu su kan kamu da ciwon sukari na nau'in biyu a cikin shekaru 10 bayan sun haifi jarirai.

Bayan da manazarta suka dauki shekaru 19 suna yin nazari kan mata kusan dari 3 da suka kamu da ciwon sukari sakamakon samun juna biyu, sun gano cewa, shayar da jariransu da nononsu ya iya rage wa mata barazanar da yawanta ya kai 40 cikin dari a fannin kamuwa da ciwon sukari na nau'in 2 a nan gaba. Kana kuma shayar da jarirai nono ya ba da tasiri kan samun daidaito a jikunan mata da yawan sukari da ke cikin jininsu a cikin gajeren lokaci.

Sabili da haka ne ma manazartan suka tunatar da cewa, matan da suka kamu da ciwon sukari sakamakon samun juna biyu, musamman ma masu dan kiba, suna iya rage fuskantar barazanar kamuwa da ciwon sukari na nau'in 2 a nan gaba ta hanyar shayar da jariransu da nononsu na tsawon a kalla watanni 3 na farko bayan haihuwar jariran. Amma ina dalilin da ya sa haka? Manazartan suna nan suna nazari.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China