in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shayar da jarirai da nonon iyaye mata ya iya rage yiwuwar fama da kiba
2013-08-02 14:25:39 cri

Masu juna biyu da suka kamu da ciwon sukari a lokacin da suke da ciki su kan haifi jarirai masu nauyi, ta yadda akasarin yaran kan yi fama da kiba. Amma sakamakon binciken baya-bayan nan da aka yi ya nuna cewa, idan iyaye mata sun shayar da jariransu da nononsu, to, za a rage wa yara yiwuwar fama da kiba.

Masu bincike na kasar Jamus sun yi bincike kan jariran da mata 324 suka haifa, wadanda suka kamu da ciwon sukari a lokacin da suke da ciki. A karshe dai sun gano cewa, a lokacin da suke kanana, jariran da ba a shayar da su da nonon iyayensu mata ba kuma nauyinsu ya zarce yadda ya kamata, yawansu ya kai kashi 37 cikin dari, yayin da suka kuma wadanda aka shayar da su da nonon iyayensu mata kuma nauyinsu ya zarce kima suka kai kashi 28 cikin dari, a cikinsu kuma, yawan wadanda iyayensu mata ba su shayar da su da nononsu har tsawon watanni 3 ba, kuma nauyinsu ya zarce yadda ya kamata ya kai kashi 32 cikin dari, amma jariran da iyayensu mata suka yi watanni fiye da 3 suna shayar da su da nononsu kuma nauyinsu ya zarce yadda ya kamata yawansu ya kai kashi 22 cikin dari.

Bayan da suka yi nazari kan dalilan wannan bambanci, masu binciken sun yanke hukuncin cewa, idan iyaye mata ba su shayar da yaransu da nononsu cikin dogon lokaci ba, to, yaransu za su iya fuskantar matsalar nauyi fiye da kima, amma idan sun shafe watanni fiye da 3 suna shayar da yaransu da nononsu, to, za a rage wa yaran rabin barazanar fama da kiba.

Masu bincike sun bayar da wannan sakamakon bincike a cikin wata mujallar kasar Amurka, mai suna 'yin jiyya ga masu sukari', wadda aka fitar da ita a kwanan baya. Kafin wannan kuma, wadannan masu bincike daga kasar Jamus sun taba gano cewa, yara na kara fuskantar yiwuwar fama da kiba, saboda iyayensu mata sun yi fama da kiba, sa'an nan kuma, jariran da aka haife su ba da dadewa ba nauyinsu ya kan wuce yadda ya kamata saboda sun yi girma a lokacin da suka kasance cikin iyayensu mata.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China