in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu abubuwan ci da ke iya taimaka man wajen kara lafiyar kwakwalwa da kuma kawar da gajiya
2013-02-06 09:18:55 cri
Ko ka kan ji kamar ba ka samu ishesshen barci ba a ko wace rana? Ko ba ka samun kakkyawan nutsuwa a yayin da kake aiki ko karatu? Ko kuma sha'awarka tana raguwa, kuma ka kan kamu da ciwon kai amma ba tare da wasu dalilai ba? To, wannan wata alama ce da ke nuna matukar gajiya a jikin mutum.

Dalilin da ya sa mutumin da ke da koshin lafiya ya kan gaji shi ne, ko bai samu lokacin da zai yi ishesshen barci ba,. Wani binciken da aka yi ya nuna cewa, mutanen da yawan su ya kai kashi 66 cikin kashi 100 suna fuskantar matsalolin yin mafarki da yawa, da rashin barci, da kuma wuyar yin shi kansa barcin. Mutanen da yawansu ya kai kashi 57 cikin kashi dari sun rasa karfin tunani sosai. An ce, idan mutum ya gaji sosai, to yana fuskantar hadarin mutuwa. Saboda haka, kamata ya yi a kara cin wasu abincin da ke iya kara karfin jikin mutum, don kawar da wannan matsalar.

Shayi na kunshe da sanadarin caffeine da ke iya taimakawa mutum wajen kara karfin numfashi, kana mutum ba zai gaji ba. Ban da Caffeine kuma, kofi da cakulefi su ma suna da amfani wajen kawar da gajiya.

Sinadaran Vitamin da ke hade da Vitamin B1, da B6, da kuma B12, da sauransu suna iya taimaka wa mutum wajen sassauta matsalar damuwa, kana da fitar da dagulan abubuwan da ke cikin jikin mutum cikin hanzari, ta yadda za su zama sinadarai masu gina jiki da ke da amfani wajen kawar da gajiya.

Sinadarin Calcium na da amfani wajen kawar da damuwa, mutanen da ke fama da matsalar rashin isashen sinadarin su kan ji gajiya. Madara da kindirmo na kunshe da sinadarin Calcium da dama, amma a yayin da ake yawaita shan abubuwan biyu, kada a manta da kara sinadarin Magnesium, cin sinadaran biyu baki daya zai taimaka wa mutum wajen kawar da gajiya.

To, masu sauraro, yanzu ga wasu abubuwan ci da ke iya taimaka man wajen kara lafiyar kwakwalwa da kuma kawar da gajiya.

Bisa tsarin likitancin gargajiyar kasar, an ce dan itacen pear na iya taimakawa wajen saurin sarrafa abinci a ciki, saboda haka cin sa na iya taimaka wa mutum wajen kara sha'awar cin abinci.

Ban da wannan kuma, innabi shi ma wani abinci ne mai kyau wajen kawar da gajiya, innabi na hade da abubuwa masu gina jiki da yawa, ciki har da Sinadarin Calcium, da sinadarin Magnesium, da sinadaran Vitamin B iri daban daban, da kuma sinadaran amino acid da yawan su ya kai 10 da jikin mutum ke bukata.

Kazalika, ruwan zuma, alayyaho, kagewa, tumatir, karas,wake, gyada, kashu, da sauransu dukkansu na da amfani waken kiyayen kwakwalwa.

Ban da haka kuma, a yayin da ake jin gajiya kada a ci naman kaza, da kifi, da kwai da yawa, wadanda ke iya kara gajiya.(Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China