in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cin kayan lambu kafin shimkafa na taimakawa wajen rage yawan sukarin da ke cikin jinin mutum
2014-03-17 09:42:06 cri

Kwanan baya, wata kungiyar nazari daga kasar Japan ta sanar da cewa, a yayin da mutum yake cin abinci, idan ya ci kayayyakin lambu, daga baya ya ci shimkafa ko taliya ko burodi da dai makamantansu, to, ko da yana fama da ciwon sukari ko a'a,hakan zai taimaka wajen rage yawan sukarin da ke cikin jininsa tare da rage karuwar yawan sukarin da ke cikin jininsa.

Mai yiwuwa ne babbar hauhawar da ake yi game da yadda yawan sukarin da ke cikin jinin mutum za ta haifar da cututtuka a jijiyoyin jinin mutum, zuciya da kwakwalwa. Imai Saeko,ya sa wata farfesa a Jami'ar Osaka ta kasar Japan ta shugabanci wata kungiyar nazari, wadda ta raba masu fama da ciwon sukari guda 19 da kuma masu koshin lafiya guda 21 zuwa sassa 2,kana ta kwatanta su tare,inda ta bukace su da su ci abinci bisa odar da aka kayyade, sa'an nan wajibi ne a yi bincike kan yawan sukarin da ke cikin jininsu a ko wadanne mintoci 5 na kwanaki 4 a jere.

Sakamakon binciken ya nuna cewa, a cikin wadanda suke fama da ciwon sukari, idan sun fara da cin shimkafa ko taliya ko burodi kafin sauran abinci,to, matsakaicin yawan sukarin da ke cikin jininsu bayan sa'o''i 2 da kammala cin abincin ya kai miligram 195 cikin mililita 100. Amma in sun fara cin wasu kayayyakin lambu kafin su ci shimkafa a yayin da suke cin abincin, to, irin wannan adadi ya kai miligram 160 cikin mililita 100. A bayyane yawan sukarin da ke cikin jininsu ya ragu kwarai da gaske, haka kuma bai sauya sosai ba.

A cikin wadanda suke da koshin lafiya kuma, an gano irin wannan sauyawar yawan sukarin da ke cikin jininsu, idan suka fara da kayayyakin lambu, kafin su ci shimkafa. Hakan ya nuna cewa, yayin da masu koshin lafiya suke cin abinci, idan suka fara da kayayyakin lambu, hakan na iya taimakawa wajen rage yawan sukarin da ke cikin jininsu.

Madam Imai Saeko ta ba da shawarar cewa, muddin aka lura da ka'idar cin abinci, alal misali, aka fara da kayan lambu, a maimakon shimkafa, to, za a iya yin rigakafin kamuwa da cututtukan da aka kamu da su sakamakon munanan hanyoyin da a kan saba bi a zaman yau da kullum.

Har wa yau kuma, dangane da cin abincin yadda ya kamata, masu nazari da ke jami'ar McMaster ta kasar Canada sun gabatar da sakamakon nazarinsu a kwanan baya cewa, cin abinci masu gina jiki yana iya rage wa masu fama da matsalolin jijiyoyin jini da ciwon zuciya barazanar sake kamuwa da ciwon ko cutar shan inna.

Masu nazarin sun nuna cewa, abinci masu gina jiki sun hada da 'ya'yan itatuwa, kayayyakin lambu, hatsi, dangin gyada da kifi. Ya fi kyau kada a ci naman sa ko tunkiya da makamantansu da kuma kwai da yawa. Ko da yake akwai bambanci a sassa daban daban a duniya ta fuskar cin abinci da kuma yawan kudin shiga, amma cin abinci masu gina jiki yana iya taimakawa wajen rage barazanar kamuwa da cututtukan jijiyoyin jini da zuciya fiye da kashi 20 cikin dari. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China