in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a wanke hannu bayan da aka je bayan gida
2014-03-10 16:43:32 cri

Masu karatu, ko kun san cewa, ranar 15 ga watan Oktoban ko wace shekara, ranar wanke hannu ce ta kasa da kasa?, Wannan ya nuna cewa, wanke hannu na da matukar muhimmanci gare mu 'yan Adam. Masu nazari daga kasar Birtaniya sun gabatar da wani sakamakon bincike a kwanan baya cewa, dimbin mutane su kan manta da su wanke hannunsu bayan da suka je bayan gida, wannan kan sa tsabar kudi da katunan bankin da ke aljihunsu su gamu da kazanta. Don haka kamata ya yi mutane su rungumi al'adar wanke hannu, musamman ma bayan da suka je bayan gida ko kuma kafin su ci abinci.

Kwalejin ilmin kiwon lafiya da cututtukan da ake samu a wurare masu zafi na jami'ar London ta Birtaniya ya gabatar da wani rahoto dake cewa, masu nazarin na jami'ar sun yi bincike kan mutane 272 mazauna biranen London, Birmingham, Liverpool da sauran manyan biranen kasar, inda suka yi bincike kan yawan kwayoyin cuta da ke kan hannayen ko wanensu, tsabar kudi da katunan bankinsu. Sakamakon binciken ya shaida cewa, an gano kwayoyin cutar Colibacillus da dangoginsu a hannayen mutanen da yawansu ya kai kashi 26 cikin dari bisa jimillar mutanen 272 da suka gudanar da binciken a kansu, sa'an nan an gano irin wadannan kwayoyin cuta a kan katunan banki da yawansu ya kai kashi 10 cikin dari da kuma tsabar kudi da yawansu ya kai kashi 14 cikin dari na wadanda wadannan mutane suke mallaka.

Kwayar cutar Colibacillus, wani nau'in kwayar cuta ce da kullum a kan same ta a cikin bayan gidan mutane ko na dabbobi ko na tsuntsaye. Idan mutane suka ci abincin da wannan kwayar cutar ta shiga, kwayar cutar ta kan shiga cikin jikin mutane, inda ta kan haddasa cututtuka daban-daban. Sakamakon binciken da masu nazarin na Birtaniya suka gabatar ya nuna cewa, yawan kwayoyin cutar Colibacillus da ke kan wasu tsabar kudin ya kusan yi daidai da yawan irin wannan kwayar cuta da ake samu a wani kazamin bayan gida.

Wanke hannu da sabulu bayan zuwa bayan gida zai taimawa wajen hana yaduwar kwayoyin cutar Colibacillus sosai. A cikin mutanen da aka yi musu binciken, wasu da yawansu ya kai kashi 91 cikin dari sun yi shelar cewa, suna wanke hannunsu bayan zuwa bayan gida. Amma yawan kwayoyin cutar da ke hannunsu da tsabar kudin da ke aljihunsu ya shaida mana cewa, hakika,abin ba haka ba ne, watakila ba su wanke hannunsu ba.

A ganin masu nazarin, sakamakon binciken ya nuna muhimmancin wanke hannu. Tsabar kudi, wani nau'in abu ne da a kan yi amfani da shi a zaman yau da kullum, kuma kwayoyin cuta masu yawan gaske da ke kansu su kan ba mutane mamaki kwarai da gaske, lamarin da ya nuna cewa, mutane da yawa su kan manta da wanke hannu bayan da suka je bayan gida.

Masu nazarin suna fatan za a yayata muhimmancin wanke hannu, a kokarin ganin mutane sun fito da kyakkyawar al'adar wanke hannu, musamman ma bayan zuwa bayan gida ko kuma kafin cin abinci.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China