in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da Faransa sun taya murnar cika shekaru 55 da kafa huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu
2019-01-27 17:14:25 cri
Yau Lahadi, shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na kasar Faransa Emmanuel Macron, sun zanta ta wayar tarho, inda suka taya juna murnar cika shekaru 55 da kafa huldar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu.

Xi Jinping ya ce, a halin yanzu, ana fuskantar damammaki da kalubaloli da dama ta fuskantar neman bunkasuwar zamantakewar al'umma. Sin da Faransa sun kasance mambobin dindindin a kwamitin sulhu na MDD, kasashen biyu na dauke da muhimmin nauyin dake wuyansu. Kasar Sin tana fatan yin hadin gwiwa da kasar Faransa wajen karfafa zumuncin gargajiya dake tsakanin kasashen biyu, sabunta fasahohin zamani bisa hadin gwiwar kasa da kasa, da kuma daga dangantakar abokantaka dake tsakanin Sin da Faransa bisa manyan tsare-tsare zuwa wani sabon matsayi, a wannan lokaci na musamman, wato yayin cika shekaru 55 da kafuwar huldar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu. Ta yadda kasashen biyu za su bada karin gudummawa a fannonin kiyaye zaman lafiya, zaman karko da neman bunkasuwar kasa da kasa.

A nasa bangare, Emmanuel Macron ya ce, ana fuskantar sauye sauyen yanayi a duniya, a matsayin zaunannun mambobin kwamitun sulhu na MDD, ya kamata kasar Sin da kasar Faransa su dukufa wajen kiyaye tsarin hadin gwiwar kasa da kasa, wanda aka tsara bisa ka'idojin mutunta juna da adalci. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China