in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Rasha da takwaransa na Faransa sun tattauna batun Syria da na Ukraine ta wayar tarho
2019-01-03 11:42:09 cri
Jiya Laraba, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da takwaransa na kasar Faransa Emmanuel Macron sun tattauna batutuwan kasar Syria da na Ukraine ta wayar tarho.

Bisa labarin da gwamnatin kasar Rasha ta fidda, an ce, shugabannin biyu sun yi tattaunawa ne kan yadda za a warware batun Syria, ta hanyar kafa wani kwamitin tsarin mulkin kasa bisa amincewar bangarorin hudu.

A ranar 17 ga watan Oktoba na shekarar 2018, shugabannnin kasashen Rasha, Faransa, Jamus da na kasar Turkiya sun cimma matsayi daya kan kafa kwamitin tsarin mulki na kasar Syria a yayin taron kolin da aka yi a birnin Istanbul, fadar mulkin kasa ta Turkiya.

Haka kuma, bisa labarin da gwamnatin kasar Rasha ta fidda, an ce, a jiya Laraba, shugaba Putin da takwaransa na kasar Faransa Emmanuel Macron sun yi musayar ra'ayoyi kan rikicin dake tsakanin kasar Rasha da kasar Ukraine.

A ranar 25 ga watan Nuwamba na shekarar 2018, rikicin dake tsakanin Rasha da Ukraine ya barke bayan kasar Rasha ta harba bindiga ga jiragen ruwan sojan kasar Ukraine guda uku a lokacin da suka tafi tekun Azov daga mashigin tekun Kerch.

Kasar Rasha ta yi zargin cewa, wadannan jiragen ruwan soja guda uku sun shiga yankin tekun kasarta. Amma gwamnatin kasar Ukraine ta ce, ta riga ta sanarwa kasar Rasha kafin zuwan wadannan jiragen ruwa a yankin, kuma a halin yanzu, ta riga ta nemi wasu lauyoyi domin ba da taimako ga wadancan mambobin jiragen ruwan sojan kasarta da kasar Rasha ta kama. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China