in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na fatan Faransa za ta kiyaye hakkin Sinawa a kasar
2017-03-28 20:10:28 cri

A Talatar nan ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana cewa, kasar Sin na lura kwarai da yadda ake bin bahasin kisan da wasu 'yan sanda farin kaya na kasar Faransa suka yi wa wani Basine dan ci rani a gidansa dake Faransa. Kuma tuni ta riga ta tuntubi kasar Faransa game da bukatar tono gaskiyar lamarin cikin hanzari, tare da daukar matakan tabbatar da tsaron lafiyar Sinawa, da kiyaye hakkinsu a Faransa.

A daren ranar Lahadi 26 ga watan nan ne 'yan sanda farin kaya na Faransa, suka harbe wani Basine dan ci rani a gidansa da ke birnin Paris. Daga baya, wasu Sinawa 'yan ci rani sun ziyarci hukumar 'yan sandan yankin domin gabatar da koken su, inda al'amarin ya kai ga barkewar rikici tsakaninsu da 'yan sandan. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China