in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin harkokin wajen Sin da Faransa sun gana kan batun zirin koriya
2017-09-01 10:57:32 cri

Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya gana da takwaransa na Faransa Jean-Yves Le Drian ta wayar tarho, game da yanayin zirin Koriya.

Wang Yi, ya jaddada matsayin kasar Sin na tabbatar da kawar da makaman nukiliya daga Zirin Koriya, tare da sukar gwajin makaman da Koriya ta Arewa ke yi.

Yayin ganawar ta su da ta gudana a jiya bisa kiran da Jean Drian ya masa, Wang Yi ya kuma yi kira ga sauran wadanda batun ya shafa, da su hada hannu wajen yayyafawa yanayin da ake cikin ruwan sanyi tare da dakatar da zaman dar-dar da ake yi yanzu nan bada jimawa ba.

A nasa bagaren, Ministan na Faransa, ya bayyana damuwar kasarsa game da gwaje-gwajen makaman nukiliya da kasar Koriya ta Arewa ke yi.

Ya kuma bayyana goyon bayansa ga kokarin da Sin ke yi na warware matsalar, ya na mai kin aminta da sukar da ake yi dake cewa kasar Sin ta gaza sauke nauyin da ke wuyanta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China