in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasashen duniya sun yi gargadi game da hadarin masu kaifin kishin kasa
2018-11-12 10:17:21 cri
An kaddamar da taron zaman lafiya na birnin Paris, a jiya Lahadi, inda Shugaba Emmanuel Macron na Faransa da Angela Markel shugabar gwamnatin Jamus da kuma Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, suka yi kira da a ci gaba da kokarin wanzar da zaman lafiya a duniya.

Bayan taron, an kuma gudanar da wani taron da ya hada gomman shugabannin kasashen duniya, a karkashin ginin The Arch of Triumph, domin tunawa da cika shekaru 100 da kawo karshen yakin duniya na 1.

Da yake Jawabi, Emmanuel Macron ya ce daukar bikin tunawa da karshen yakin duniya na farko a matsayin alamar zaman lafiya mai dorewa tsakanin kasashe, ko kuma matakin karshe na hadin kai kafin duniya ta kuma tsunduma cikin wata sabuwar matsala, abu ne da ya dogara a kan su shugabanni.

A nasa bangaren, Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya ce akwai abubuwa da dama a yanzu da suka yi kama da farkon karni na 20 da na 1930, yana mai gargadi game da hadarin rarrabuwar kawuna saboda siyasa da ma rarrabuwar al'umma da kanta.

Ya kuma yabawa manufar MDD, yana mai cewa, a yanzu, ita ce cibiyar dake kokarin samar da zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a duniya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China