Zuwa tsakar ranar jiyan, mutane 36,500 ne suka shiga zanga-zangar a fadin Faransa, ciki har da 5,500 da suka yi a babban birnin kasar, idan aka kwatanta da 106,300 da suka fito a ranar Asabar din makon da ya gabata.
Hotunan bidiyo sun nuna yadda hayaki mai sa hawaye ya turnuke sararin samaniya a saman ginin tarihi na L'Arc de Triomphe, inda aka fara samun arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanga da misalin karfe 8 na safe agogon GMT, bayan wata tawagar ta yi kokarin kutsawa inda jami'an tsaro suka killace.
'Yan sanda sun mayar da martani ne da hayaki mai sa hawaye, da gurneti mara kisa da kuma harsasan ruwa, domin tarwatsa masu zanga zangar a wani sabon rikicin da ya kai ga raunana mutane 20, ciki har da 'yan sandan kwantar da tarzoma 6. (Fa'iza Mustapha)