in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Macron ya yi Allah wadai da mummunan tashin hankalin da ya barke a lokacin zanga zangar kasar
2019-01-06 16:51:06 cri

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya wallafa a shafinsa na tiwita a jiya Asabar, inda ya yi Allah wadai da abin da ya kira mummunan tashin hankali na zanga zangar da aka yiwa lakabi da "yellow vest" wanda mutane sama da dubu 50 suka yi gangami a duk fadin kasar.

"Bugu da kari, mummunan tashin hankali ya tasowa kasarmu, da masu tsaron kasar, da wakilan kasar, har ma da turar kasar. Wadanda ke kokarin ruruta wutar wannan tashin hankali sun manta da kishin wannan kasa da hakkin kasar. Dole ne za'a yi adalci. Dole ne kowa da kowa ya shiga cikin muhawarar tattauna hanyoyin warware rikicin kasar," Macron ya wallafa a shafinsa na tiwita.

A Paris, masu zanga zangar sun kai kimanin 3,500, sun ninka adadin mutane 800 da suka shiga zanga zangar a makon jiya.

Da yammacin ranar Asabar, tashin hankali ya barke a lokacin da wasu daga cikin masu zanga zangar suka yi amfani da wasu motocin aikin gine gine a birnin Paris, inda suka barnata wasu kofofin katako na wani ginin gwamnati a yayin da suke yunkurin shiga harabar ginin. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China