in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Faransa za ta kaddamar da bayani game da harbe wani Basine
2017-03-29 19:44:33 cri

A Larabar nan ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana cewa, ministocin ma'aikatar harkokin wajen kasar Faransa, da na ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar sun bayyana cewa, za su gaggauta bin bahasin harbe wani Basine dan ci rani da 'yan sandan farin kaya na kasar suka yi, tare da tabbatar da fayyace gaskiyar lamarin ba tare da bata lokaci ba.

A daren ranar Lahadi 26 ga watan nan ne 'yan sandan farin kaya na Faransa, suka harbe wani Basine dan ci rani a gidansa da ke birnin Paris. Daga baya, wasu Sinawa 'yan ci rani suka ziyarci hukumar 'yan sandan yankin domin gabatar da kokensu, inda al'amarin ya kai ga barkewar rikici tsakaninsu da 'yan sandan. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China