in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Faransa za su daga matsayin dangantakar dake tsakaninsu
2018-01-10 10:57:15 cri

A ranar Talata, kasashen Sin da Faransa suka cimma matsaya na kara daga matsayin dangantakar dake tsakaninsu.

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron, sun cimma wannan matsaya ne a lokacin tattaunawar da suka gudanar a Beijing.

Xi ya bayyana cewa, Macron shi ne shugaban kasa na farko da ya ziyarci kasar Sin tun bayan shigowar shekarar 2018, kana shi ne shugaban kasa daga nahiyar Turai na farko da ya ziyarci kasar ta Sin tun bayan kammala babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta CPC mai mulkin kasar karo na 19.

"An fara sabuwar dangantaka tsakanin kasashen biyu," in ji shugaba Xi. "Kasar Sin a shirye take ta daga matsayin mu'amala da amincewa da juna, da hadin gwiwa tsakanin Sin da Faransa, domin samar da gagarumin cigaba wajen daga matsayin dangantakar dake tsakanin kasar Sin da Faransa."

"Kasar Sin da Faransa, mambobi ne na dindindin a kwamitin sulhun MDD, kuma manyan kasashen duniya ne, don haka wajibi ne su yi hadin gwiwa tare da juna don sauke nauyin dake wuyansu", in ji Xi.

Xi ya ce, akwai bukatar Sin da Faransa su hada hannu domin tallafawa wajen tafiyar da al'amuran duniya, kuma su bude kofa ga sha'anin ci gaban tattalin arzikin duniya, kuma su yaki duk wani batun da ya shafi nuna wariya, kuma su ingiza cigaban tattalin arzikin duniya gaba ta hanyar bude kofa, da samar da daidaito, da cimma moriyar daga dukkan bangarori.

A nasa bangaren, Macron, ya bayyana cewa, a matsayinsu na kasashe biyu masu wakilcin dindindin a kwamitin sulhun MDD, akwai babban nauyin dake wuyansu na samar da tsaro a duniya. Ya kara da cewa, Faransa da Sin suna tafiyar da kyakkyawar mu'amalar dake tsakaninsu wajen samar da cigaban duniya da kuma kokarin yaki da matsalar sauyin yanayi a duniya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China