Sai dai Sergei Lavrov da ya bayyana haka jiya a Astana babban birnin kasar Kazakhstan, bai yi wani karin bayani da ya shafi korar jami'an diflomasiyyar Burtaniya daga kasarsa ba.
Ministocin harkokin wajen kasashen Rasha da Turkiya da kuma Iran, sun gana jiya a birnin Astana kan batun Syria. Kuma a yayin taron manema labarai da aka yi bayan ganawar tasu ne Mr. Lavrov ya bayyana cewa, zargin da Burtaniya ta yi wa kasarsa na sanyawa 'dan leken asiri Sergei Skripal da 'yar sa guba, wani sabon mataki ne da aka dauka na nuna adawa ga Rasha . (Maryam)