Shoygu ya bayyana hakan ne a birnin Moscow, fadar mulkin kasar Rashar, inda ya ce, wannan niyya ce da shugaba Vladimir Putin na kasar ya riga ya tsayar da ita. A cewarsa, shirin tsakaita bude wutar ya fara ne daga ranar 27 ga watan da muke ciki, za a gudanar da tsagaita bude wuta tsakanin karfe 9 har zuwa karfe 2 da rana, don ba da damar gudanar da ayyukan jin kai. Ban da haka kuma, za a bude wata hanya ta musamman a yankin Guta na Gabas domin fararen hula su bi wannan hanya su tsira.
Yankin Guta na Gabas ya kasance a karkara dake gabashin birnin Damascus, fadar mulkin kasar Syria. Wasu dakaru masu kin jinin gwamnati sun kwace ikon yankin a shekarar 2012, daga bisani sojojin gwamati sun kewaya wurin har tsawon shekaru 5, amma har zuwa yanzu ba su samu damar shiga cikin yankin ba.(Bello Wang)