Ma'aikatar kudi ta kasar Amurka ta sanar jiya Alhamis cewa, za ta sanya wa kamfanonim Rasha 5 da wasu 'yan kasar 19 takunkumi, bisa zargin cewa, sun yi kutse ta Intanat, ciki har da yunkurin kawo cikas ga babban zaben kasar Amurka na shekarar 2016.
Wata sanarwar da sakataren kudin Amurka Steven Mnuchin ya bayar ta bayyana cewa, Amurka ta dauki wannan mataki ne domin mayar da martini ga Rasha kan kutsen da ta yi. A nan gaba kuma ma'aikatar za ta fitar da karin matakan takumkumin, a kokarin hana jami'an gwamnatin Rasha da suka yiwa harkokin kudin kasar babakere. Ya kuma jaddada cewa, Rasha za ta yi hasara sakamakon munanan ayyukan da suka aikata.
Bisa ka'ida, za a haramtawa mutane da kamfanonin da aka kakabawa takumkumi taba kadarorinsu, sa'an nan an hana Amurkawa su yi duk wata mu'amular cinikiyya tare da su.(Kande Gao)