Wani jirgin saman fasinjan kasar Rasha kirar Antonov-148 dauke da mutane 71 ya fado jim kadan da tashinsa daga filin jiragen saman kasar Moscow. Inda ake fargabar dukkan fisinjoji da ma'aikatan jirgin sun mutu.
Wata majiyar agajin gaggawa da shaidawa kamfanin dillancin labarai na Interfax na kasar ta Rasha cewa, jingin dauke da fasinjoji 65 da ma'aikatansa guda 6 yana kan hanyarsa ce ta zuwa Orsk dake yankin Orenburg na yammacin kasar daga filin jirgen sama na Domodedovo dake birnin Moscow.
An daina jin duriyar jirgin ne da misalin karfe 4.21 na yamma agogon Rasha, 'yan mintoci bayan tashinsa. Kuma shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa, jirgin ya fado ne a kusa da kauyen Argunovo, kuma ya kama da wuta ne tun yana sama. Yanzu haka dai an gano sassan wasu gawawwaki guda biyu a wurin da hadarin ya faru.(Ibrahim)