Wata sanarwa da ma'aikatar ta dora kan shafin ta na yanar gizo, ta yi kakkausan suka game da furucin firaministar Birtaniya Theresa May, na zargin Rasha da sanyawa 'dan leken asiri Sergei Skripal da 'yar sa guba. Rasha ta kuma alkawarta daukar matakin gaggawa na hukunci kan hakan.
Sanarwar ta ce kalaman firaminista Theresa May na ranar 14 ga wata sun sabawa ka'idar zaman jituwa dake wanzuwa tsakanin kasashen biyu.
Sanarwar ta kara da cewa, sakamakon amfani da hanyar bincike maras tsari, Birtaniya ta sake daukar mataki na nuna kin jinni ga Rasha. Har wa yau Rasha ta ce ba za ta lamunci matakan da Birtaniya ta fara dauka a kan ta ba, wadanda ke da nasaba da cimma muradun siyasa masu kunshe da nuna tsana da muzugunawa, ciki hadda matakin korar jami'an diflomasiyyar Rasha su 23 daga Birtaniya.
Daga karshe sanarwar ta tabbatar da cewa, Rasha za ta gaggauta daukar matakan ramuwar gayya ba tare da wani jinkiri ba. (Saminu)