Ma'aikatar ta ruwaito cewa, jirgin ya fadi ne yayin da yake neman sauka, kuma inda ya fadi na da tazarar mita 500 daga titin jirgi. An ce, jirgin na dauke da fasinjoji 26 tare da ma'aikatansa 6, wadanda gaba daya suka gamu da ajalinsu.
Kwarya-kwaryar bincike ya nuna cewa, akwai yiwuwar jirgin ya fadi ne sakamakon matsalar na'urar. A cewar ma'aikatar tsaron, jirgin bai gamu da wani hari ba, kuma za ta gudanar da bincike a kan hadarin. (Lubabatu)