An ce jaririn mai suna Logan Gomes, na cikin wadanda suka kone yayin gobarar. Kaza lika rahoton ya bayyana Victoria King, da 'yarta Alexandra Atala, a matsayin mutane biyu na karshe da suka hallaka a yayin gobarar.
Rundunar 'yan sandan ta ce an riga an sanar da iyalan mutanen 71 sakamakon binciken da aka gudanar, ana kuma tallafa musu da matakan kwantar da hankali karkashin wani shiri na musamman.
Rahoton da 'yan sandan suka fitar ya kuma nuna cewa, an samu kimanin tan 15.5 na baraguzai a kowane hawa na babban ginin mai hawa 24, yayin da kuma ake ci gaba da gudanar da nazarin kimiyya, domin gano asalin daukacin wadanda wannan hadari ya rutsa da su.
'Yan sandan birnin na London, na ran kammala binciken da suke aiwatarwa nan gaba cikin watan Disamba dake tafe. (Saminu Hassan)