in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakiliya ta musamman ta shugaban kasar Sin ta gana da sabon shugaban Laberiya
2018-01-24 11:03:17 cri
A jiya Talata ne, wakiliya ta musamman ta shugaban kasar Sin Xi Jinping, wadda kuma ita ce babbar darektar kwamitin kula da harkokin kiwon lafiya da kayyade iyali na kasar, Madam Li Bin, ta gana da sabon shugaban kasar Laberiya, George Weah a birnin Monrovia.

Madam Li ta isar da sakon taya murna da fatan alheri na shugaba Xi Jinping zuwa ga George Weah, inda ta ce, tun da kasashen biyu suka farfado da huldar jakadancinsu a shekara ta 2003, ya zuwa yanzu, Laberiya ta tsaya kan manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duk fadin duniya, ita ma kasar Sin na nuna goyon-baya ga Laberiya wajen sake farfado da harkokin kasar, har ma alakar kasashen biyu da hadin-gwiwarsu sun bunkasa yadda ya kamata, abun da ya kawo moriya ga al'ummarsu. Kasar Sin na maida hankali sosai kan raya hulda da Laberiya, kana, tana fatan yin kokari tare da gwamnatin Laberiya dake karkashin shugabancin Weah, domin ciyar da huldodin kasashen biyu gaba.

A nasa bangren, George Weah yana mai cewa, tsayawa kan manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duk duniya, ita ce muhimmiyar manufa ta sabuwar gwamnatin Laberiya, kana, kasarsa na fatan kara habaka dangantakar abokantaka mai karfi tare da kasar Sin.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China