in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar zaben kasar Liberia ta sanar da dan takarar jam'iyyar adawa a matsayin zababben shugaban kasar
2017-12-30 12:33:18 cri

Hukumar zaben kasar Liberia, ta ayyana George Weah, dan takarar jam'iyyar adawa ta Coalition for Democratic Change CDC, a matsayin zababben shugaban kasar, bayan ya lashe zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da aka gudanar ranar Talata da ta gabata.

Yayin wani taron manema labarai jiya a Monrovia, Shugaban hukumar Jerome Korkoya, ya ce George Weah ya samu kaso 61.5 na kuri'un da aka kada, inda ya samu jimilar kuri'u 732,185 yayin da Joseph Boakai mataimakin shugaban kasar mai ci kuma dan takarar Jam'iyyar Unity mai mulkin kasar, ya samu kaso 38.5 kuri'un da aka kada, inda ya samu kuri'u 467,579.

Jimilar mutane 1,218,124 ne suka kada kuri'a a zagaye na biyu na zaben da aka jinkirta gudanar da shi.

Jerome Korkoya ya ce kamar yadda kundin tsarin kasar ya tanada, hukumar zaben za ta bada shaidar nasarar lashe zabe ga George Weah da abokiyar takararsa Jewel Howards Taylor, tsohuwar matar tsohon shugaban kasar, cikin kwanaki 7 masu zuwa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China