Mr. Korkoya ya ce wannan sakamako na zuwa ne yayin da aka riga aka kidaya kaso 98.1 na daukacin kuri'un da aka kada. Mr. Weah dai ya kai ga samun kuri'u har kaso 61.5 bisa dari, yayin da Joseph Boakai ke da kaso 38.5 bisa dari na jimillar kuri'un da aka kada.
George Weah, tsohon tauraron kwallon kafar kasar ta Liberia, ya lashe kuri'un gundumomi 14 cikin 15 dake sassan kasar. Kuma hukumar zaben kasar ta ce adadin masu kada kuri'unsu a kasar ya kai kaso 56 bisa dari. Ana kuma sa ran fidda sakamakon karshe na zaben a Juma'ar nan. (Saminu Hassan)