in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Nijeriya ya jinjinawa gudanar zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Liberia da cikin kwanciyar hankali da lumana
2017-12-30 12:36:23 cri

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Liberia da ya gudana lami lafiya a matsayin kari ga nasarar tsarin demokradiyyar nahiyar Afrika.

Cikin wata sanarwa da aka fitar jiya Juma'a, Shugaba Buhari ya yabawa al'ummar Liberia bisa gudanar da zaben cikin lumana, wanda ya zama karo na farko tun bayan shekarar 1944 da aka sauya mulkin kasar cikin kwanciyar hankali da lumana.

Muhammadu Buhari ya taya George Weah murnar lashe zaben, kana ya yabawa kokarin hukumar zaben kasar da kuma masu sanya ido na yankin da na kasashen waje, wadanda ya ce sun bada gudunmuwa ga harkokin zaben tare da kawar da rikicin bayan zabe a kasar dake yammacin Afrika.

Har ila yau, Shugaban na Nijeriya ya bayyana nasarar George Weah a matsayin tabbaci dake nuna kudurin al'ummar kasar na kasancewa cikin hadin kai da zaman lafiya da ci gaba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China