in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rantsar da sabon shugaban Laberiya George Weah
2018-01-23 09:40:00 cri

An rantsar da George Weah a matsayin sabon shugaban kasar Laberiya a filin wasannin motsa jiki na SKD dake birnin Monrovia jiya Litinin.

Yayin da yake gabatar da jawabi a wajen bikin rantsuwar kama aiki, Weah ya ce, a cikin wa'adin aikinsa, zai yi namijin kokarin jagorantar gwamnatinsa wajen biyan bukatun al'ummar kasar.

Weah ya kuma nuna godiya ga kasashe da kungiyoyin kasa da kasa, wadanda suke nuna goyon-baya da taimako ga Laberiya, ya kuma alkawarta cewa, zai ci gaba da karfafa zumunci tsakanin kasarsa da sauran kasashen duniya.

Game da dangantakar Laberiya da Sin, George Weah ya sake jaddada cewa, Laberiya za ta tsaya kan manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, kuma gwamnatinsa za ta yi aiki kafada da kafada tare da gwamnatin kasar Sin.

Weah ya lashi takobin kara kokarinsa wajen karfafa dangantaka da hadin-gwiwa tsakanin kasarsa da kasar ta Sin.

Wakiliya ta musamman da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tura zuwa Laberiya, wadda ita ce darektar kwamitin kula da harkokin kiwon lafiya da kayyade iyali na kasar Sin Madam Li Bin ta halarci bikin rantsar da George Weah. Kaza lika shugabanni da kuma wakilai daga kasashen Najeriya, Saliyo, Guinea, Kwadibwa, Togo, Gabon, Ghana, Senegal su ma sun halarci bikin.

A ranar 28 ga watan karshe na shekarar da ta shude, kwamitin zabe na kasar Laberiya ya sanar da cewa, tsohon gwarzon wasan kwallon kafar duniya George Weah, mai shekaru 51 da haihuwa, ya lashe babban zaben shugabancin kasar.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China