in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zababben shugaban kasar Liberia ya sha alwashin cika alkawuran zabe
2018-01-05 09:50:43 cri
Zababben shugaban kasar Liberia George Weah, ya sha alwashin cika alkawuran da ya dauka yayin yakin neman zaben sa. George Weah ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis, yana mai tabbatar wa al'ummar kasar cewa zai baiwa marada kunya.

Shugaban mai jiran gado ya kuma yi kira ga 'yan kasar da su rungumi manufofin raya kasa, da amincewa tare da fahimtar juna.

Mr. Weah dai na shirin shan rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban Liberia na 25. A jiya Alhamis ne kuma hukumar zaben Liberia ta damka masa takardar lashe zaben shugabancin kasar na shekarar 2017.

An gudanar da kwarya kwaryar bikin mika takardar shaidar ga Mr. Weah ne a helkwatar hukumar zaben kasar dake garin Sinkor a wajen birnin Monrovia. George Weah ya halarci taron tare da mataimakiyar sa Jewel Howard-Taylor, da kuma zababbun 'yan majalissar dokokin kasar da aka zaba a ranar 10 ga watan Oktoba.

Da yake mika takardar shaidar lashe zaben, shugaban hukumar zaben Liberia ya ce shaidar na nuna cikakken halascin sabbin jagororin kasar ne da aka zaba.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China