in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kori Ellen Johnson Sirleaf daga jam'iyyarta
2018-01-15 10:41:55 cri

Jiya Lahadi, jam'iyyar Unity mai mulki a kasar Laberiya, ta sanar da cewa, ta kori shugabar kasar mai barin gado, Ellen Johnson Serleaf daga jam'iyyar, saboda ba ta goyi-bayan dan takarar jam'iyyar ba a zaben shugabancin kasar da aka yi kwanan baya. A cewar jam'iyyar Unity, abun da Sirleaf ta yi, ya sabawa ka'idojin jam'iyyarta.

Mai magana da yawun jam'iyyar Unity ta Laberiya Mohammed Ali ya tabbatar da cewa, jam'iyyar ta kori Sirleaf a daren ranar Asabar din da ta gabata. Mohammed Ali ya kara da cewa, Joseph Boakai shi ma ya goyi-bayan korar tata. Haka kuma an kori wasu manyan jami'an gwamnati dake goyon bayan Sirleaf daga jam'iyyar ta Unity.

Ellen Johnson Sirleaf ta rike shugabancin kasar Laberiya har sau biyu, kuma za ta kammala wa'adinta ne a karshen watan da muke ciki. Har yanzu dai Sirleaf ba ta ce uffan ba game da korar da jam'iyyar Unity ta yi mata.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China