in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabar kasar Laberiya ta jinjinawa bankin AfDB
2016-03-13 13:52:01 cri
Shugaba Ellen Johnson Sirleaf ta Laberiya, ta jinjinawa irin kokarin da bankin raya Afirka ko AfDB ke yi, wajen samar da ci gaba a nahiyar Afirka tun daga shekarun 1960 kawo yanzu.

Shugabar ta yi wannan tsokaci ne yayin da ta karbi bakuncin shugaban bankin na AfDB Akinwumi Adesina a birnin Monrovia, fadar mulkin kasar ta Laberiya. Wata sanarwa da fadar gwamnatin kasar ta fitar ta rawaito shugaba Sirleaf na cewa duk da faduwar farashin roba da karfe da kasar ke tinkaho da su wajen samun kudin shiga, a daya hannu kasar na godiya game da irin gagarumin taimako da take sama daga bankin na raya Afirka.

Kaza lika shugaba Sirleaf ta bayyana aniyar kasar ta game da fadada hanyoyin bunkasa tattalin arziki, kwatankwacin irin wadanda Mr. Adesina ya aiwatar lokacin yana ministan ma'aikatar gona a tarayyar Najeriya.

A nasa bangare Mr. Adesina ya bayyana jagorancin shugaba Sirleaf, a matsayin muhimmin jigon samar da daidaito a fannin siyasar kasar. Har ila yau a madadin bankin AfDB ya alkawarta ci gaba da baiwa Laberiya tallafin duk da ya dace, ciki hadda na bunkasa fannin makamashi da noma. Bugu da kari Adesina ya ce a yanzu haka bankin sa na tallafawa shirye shirye 17 a kasar ta Laberiya, wadanda suka hada da na bunkasa samar da makamashi, da ababen more rayuwa, da sufuri, da samar da ruwa da kuma tsaftar muhalli.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China