in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An baiwa rukunin masu aikin jiyya na kasar Sin dake Laberiya lambar yabo
2016-07-25 11:25:52 cri

An kaddamar da bikin mika lambar yabo ta "Golden Image Award" ta shekarar 2016 a Monrovia hedkwatar kasar Laberiya. Inda mataimakin shugaban kasar Mista Joseph Nyuma Boakai, ya baiwa runkunin masu aikin jiyya na kasar Sin wannan lambar yabo, don nuna karbuwa ga aikin da suka yi na yaki da cutar Ebola. A madadin dukkanin mambobin rukunin masu aikin jiyya na kasar Sin zagaye na 9, madam Sun Lijuan ta karbi wannan lambar yabo.

Rahotanni sun bayyana cewa, an fara ba da irin wannan lamba ta yabo ne tun daga shekarar 2011, inda kuma a ko wace shekara ake baiwa wannan lamba ga wadanda suka taka rawar gani a fannoni daban-daban ga kasar ta Laberiya, a matsayin daya daga cikin wasu ayyuka na taya murnar samun 'yancin kan kasar.

Shugabanni da kuma wakilan bangarori daban-daban na dora muhimmanci sosai ga wannan biki, don haka ne ya yi matukar suna a Laberiya. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China