in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta hada hannu da Mozambique wajen yaki da masu cinikin namun daji ba bisa ka'ida ba
2017-11-25 13:49:42 cri
Hukumomin kare halittu dake fuskantar barazanar karewa a doron kasa na kasar Sin da na Mozambique, da wasu hukomomin amfani da dokokin da batun ya shafa, sun gudanar da wani taro a birnin Maputo, fadar mulkin kasar Mozambique.

A yayin taron, sun tsai da kudurin hada gwiwa domin yaki da masu aikata laifuffukan cinikin namun daji ba bisa doka ba a tsakanin kasa da kasa.

Wakiliyar kasar Sin a ofishin kula da harkokin shige da ficen halittu dake fuskantar barazanar karewa a doron kasa Xiao Hong ta bayyana cewa, ya kamata masu ruwa da tsaki su hada kai wajen yaki da masu cinikin namun daji ta haramtacciyar hanya, inda ta ce ya kamata a dauki matakan ragewa ko kuma kawar da bukatun mutane kan namun daji, sa'an nan, a karfafa ayyukan sa ido kan harkokin cinikinsu, domin hana safarar dabbobin daji ba bisa ka'ida ba tsakanin kasa da kasa.

Ta kara da cewa, dole ne a karfafa ayyukan kare namun daji a kasashen duniya, ta yadda za a rage adadin masu sayar da namun daji ba bisa doka ba.

Bugu da kari, ta ce, ya kamata a ci gaba da hada hannu tsakanin hukumomin kasar Sin da na kasashen waje, domin yaki da wadanda suke aikata wannan laifi. Haka kuma, ana bukatar goyon baya daga al'ummomin kasa da kasa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China