in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun sojin Malawi sun haifar da zaman dar dar bayan da suka tsallaka iyakar kasar Mozambique
2017-10-04 12:36:01 cri
Rundunar 'yan sandan kasar Mozambique, ta ce dakarun sojin kasar Malawi dake tsaron kan iyakar kasashen biyu, sun tsallaka iyaka zuwa wani yanki na Mozambique, suka kuma yi harbi sama, lamarin da ya tsorata mazauna yankin, tare da haifar da yanayi na dar dar.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin na ranar Alhamis din da ta gabata, kwamandan 'yan sandan lardin Niassa, Aquilasse Kapangula, ya ce dakarun na Malawi sun ketare wani yanki na masunta dake gundumar Chiuta a lardin, bayan kuma sun yi harbin ne suka koma sansanin su ta wani jirgin ruwa.

Mr. Kapangula wanda ya shaida hakan a birnin Lichinga fadar mulkin lardin na Niassa, ya ce burin dakarun sojin Malawin shi ne korar masuntan wannan yanki 'yan Mozambique dake sana'ar su a yankin.

Ba dai wannan ne karon farko da ake samun yanayi na zaman doya da man ja tsakanin kasashen biyu game da rikicin kan iyaka ba. A shekarar 2015 ma, ta kai ga sai da wakilan gwamnatocin biyu suka tattauna game da batun shata kan iyaka, da na gina matsugunan al'umma, tare da bude filayen noma a yankin kan iyakar da ake takaddama a kan sa.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China