A yayin ziyarar, tawagar kafofin watsa labaru ta kasar Mozambique ta ziyarci wasu kamfanonin sarrafa amfanin gona, da cibiyar binciken fasahohin noma, da wurin adana kayayyakin tarihi na aikin gona, inda suka samu damar ganewa idanunsu yadda kasar Sin take kokarin zamanintar da fasahar aikin gona.
Haka zalika, mambobin tawagar sun ziyarci ofishin jaridar Heilongjiang Daily, inda suka tattauna kan matakan da za a bi don karfafa hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin 2 a fannonin aikin watsa labarai da al'adu.
A cewar Madam Emilia Jubileu Moiane, kasar Mozambique tana da makeken fili, amma ba ta da fasahohin zamani na sarrafa amfanin gona, irin na lardin Heilongjiang na kasar Sin. Saboda haka, suna fatan ganin kasashen 2 za su kara yin hadin gwiwa a bangarorin da suka hada da shuka hatsi, da sarrafa amfanin gona, tare da habaka mu'amala a fannin al'adu, da zurfafa hadin gwiwa tsakanin hukumomin al'adu, da kafafen watsa labaru, na kasashen 2.(Bello Wang)