A bara dai, kasar Sin ta yi kokari matuka wajen sa ido kan masu shigo da hauren giwa gami da kayayyakin dake da nasaba da shi cikin kasar, da tsawaita wa'adin haramta shigar hauren giwa gida na wucin gadi. Har wa yau kuma, hukumar kula da harkokin gandun dajin kasar Sin ta dauki wasu tsauraran matakai a fadin kasar, na yakar laifuffukan da ke nasaba da cinikin namun daji ba bisa doka ba.
A wani labarin kuma, yayin da yake zantawa kan batutuwan da za'a kara maida hankali a kai a bana, mataimakin sashin bada kariya na hukumar kula da harkokin gandun dajin kasar Sin Wang Weisheng ya ce, Sin za ta ci gaba da kyautata wasu tsare-tsaren da suka shafi dokar kare namun daji, da himmatuwa wajen yakar cinikin namun daji ba bisa doka ba.(Murtala Zhang)