Mataimakin darakta a hukumar kula da gandun daji ta kasar Chen Fengxue ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, yayin bikin kaddamar da gidan killace namun dajin garin Changsha dake lardin Hunan.
Mr. Chen ya kara da cewa, samar da wadannan gidaje zai kara tabbatar da aniyar gwamnatin kasar Sin na bada kariya ga namun daji, da ilmantar da al'umma, tare da bada damar gudanar da bincike game da hakan, yayin da a hannu guda, matakin ke nuni ga irin nasarar da kasar ta samu a fannin yaki da masu fataucin sassan namun daji ba bisa ka'ida ba.(Saminu)