in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta sha alwashin kiyaye gandun daji a nahiyar Afrika
2017-05-04 11:00:17 cri

Kasar Sin ta yi ikirarin tallafawa nahiyar Afrika wajen aikinta gandun daji, mahukuntan kasar Sin ne suka bayyana hakan a jiya Laraba yayin taron kwamitin shari'a na tuntuba na nahiyar Asiya da Afrika wato Asian-African Legal Consultative Organization ko kuma (AALCO) a takaice.

Meng Xianlin, shi ne babban daraktan ofishin kiyaye gandun dabbobi mai kula da shigi da fici na kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin a shirye take ta agazawa kasashen Afrika wajen hukunta masu alkata laifukan hallaka namun daji.

Meng ya ce, dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika, ba kawai ta shafi mu'amalar tattalin arziki ba ne, har ma ta shafi batun kiyaye gandun daji.

Gwamnatocin kasashen Sin da Kenya ne suka jagoranci shirya shirin yaki da haramta cinikin dabbobin daji ba bisa ka'ida ba domin martaba dokoki a lokacin taron dandalin AALCO karo na 56.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China