in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Interpol ta kame mutane 376 dake farautar namun daji a Afrika
2015-12-23 09:41:50 cri

A wani samame da nufin kame masu farautar hauren giwaye da na bauna ya kawo nasarar kame mutane 376, aka kuma kwace tan 4.5 na kayayyakin namun dajin a daukacin fadin Afrika .

A cikin sanarwa da hukumar 'yan sandan duniya Interpol ta fitar ranar Talatan nan ta ce, samamem mai suna Worthy II ya kunshi kasashen Afrika 11 da suka hada da Habasha, Kenya, Malawi, Mozambique, Namibiya, Afrika ta kudu, Sudan, Swaziland, Tanzaniya, Uganda da kuma Zambiya.

Wannan aiki ya kawo nasarar kwace bawon dabbar Pangoli 2,029, kunkuru masu rai 173, da kuma harsasai 532, da manyan bindigogi 5 da bindiga kirar hannu 2 da sauran kayayyaki, in ji hukumar dake da cibiya a Lyon a sanarwar da ta fitar wa manema labarai.

Daga watan Janairun wannan shekarar, shirin samamen na tsawon watanni 10 na da nufin inganta hadin gwiwwa wajen tabbatar da kiyaye doka a kan laifuffukan da suka shafi namun daji ta tsallaken iyakokin kasashe, hadin gwiwwa da hukumomi, musanyar sakamakon binciken sirri da tantancewa, a cewar sanarwar.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China