in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da Amurka don karfafa ayyukan hana fataucin hauren giwaye
2016-01-26 11:12:42 cri

Ma'aikatar muhalli da albarkatun kasa ta kasar Kenya ta rattaba hannu a kan yarjejeniyar fahimtar juna tare da gwamnatin kasar Amurka don inganta ayyukanta na yaki da laifuka a kan namun daji a kasar dake gabashin Afrika.

Sakatariyar Amurka a kan harkokin cikin gida Sally Jewell da yanzu haka take ziyarar aiki a kasar ta Kenya tare da sakaraten gwamnatin kasar Kenya a kan harkokin muhalli da albarkatun kasa Farfesa Judi Wakhungu suka shaida bikin rattaba hannun a wannan sabuwar yarjejeniya domin karfafa kokarin gwamnati a yakin da take na fataucin namun daji.

A cikin jawabin da ta gabatar wajen bude bikin, Madam Jewell ta ce Amurka za ta samar da taimakon fasaha da zai taimaka ma Kenya wajen magance fataucin da ke zama barazana ga rayuwar namun daji kamar su giwaye da bauna.

Ta ce sabuwar yarjejeniyar fahimtar juna za ta tabbatar da aiki tsakanin gwamnatocin kasashen biyu wajen dakile laiffuffukan da suka shafi namun daji kwarai da gaske. Sannan ta bayyana cewa, a cikin sabuwar yarjejeniyar za a mai da hankali ne a kan taimakon fasaha da horas da jami'ai da samar da kudaden da zai taimaka a inganta sa ido a tashar jirgin ruwa ta Mombasa.

Kasashen Amurka, Sin, da mambobin kasashen Tarayyar Turai sun karfafa hadin gwiwwarsu da Kenya a bangaren kare namun daji.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China