in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mozambique ta amince da yarjejeniyar Paris game da sauyin yanayi
2017-11-09 10:22:24 cri
A ranar Laraba majalisar dokokin kasar Mozambique ta amince da yarjejeniyar Paris game da sauyin yanayi.

An rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris ne a babban taron kasa da kasa game da sauyin yanayi (UNFCCC) karo na 21 a birnin Paris wanda aka cimma matsaya kansa tun a shekarar 2015.

Mamba a majalisar dokokin kasar ta Mozambique ya bayyana cewa, amincewa da kuduri ya biyo bayan cimma matsaya ne da aka samu tsakanin bangarori uku dake jagorancin majalisar dokokin kasar ta Mozambique.

Mozambique za ta gabatar da bayananta da kuma gudumawarta game da matakan da za ta dauka wajen rage gurbatar yanayi na shekaru biyar-biyar.

Karkashin yarjejeniyar ta Paris za'a rage karuwar gurbatar yanayi da kasa da degree 2 a ma'aunin Celsius. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China