Unicom da Huawei sun kulla jarjejeniyar gina wayoyin sadarwa a karkashin kudancin tekun Atlantic
Kwanan baya, kamfanin Unicom na kasar Sin, da kamfanin sadarwa na kasar Kamaru wato CAMTEL da kuma kamfanin Huawei sun kulla wata jarjejeniyar gina wayoyin sadarwa cikin hadin gwiwa a karkashin kudancin tekun Atlantic, wato yarjejeniyar SAIL a birnin Shanghai na kasar Sin.
Kasar Kamaru tana ganin cewa, aikin shi ne muhimmin ci gaba da kasar za ta samu wajen raya harkokin sadarwa na zamani.
Gaba daya, tsawon SAIL zai kai kimanin kilomita dubu 6, wanda zai hada hanyoyin sadarwa a tsakanin nahiyar Afirka da nahiyar Amurka ta kudu, wanda zai samar da wayoyin sadarwa mafi kyau a tsakanin nahiyoyin biyu. (Maryam)